Home Labarai PDP Ta Kafa Kwamitin Tantance Masu Takarar Mataimakin Shugaban Ƙasa

PDP Ta Kafa Kwamitin Tantance Masu Takarar Mataimakin Shugaban Ƙasa

575
0

Jam’iyyar PDP ta kafa kwamitin mutane 12 da za su tantance masu takarar kujerar mataimakin shugaban ƙasa a zaɓen shekara ta 2023.

Sakataren Yaɗa Labarai na jam’iyyar PDP na Ƙasa Ɗebo Ologunagba ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar, inda ya ce za a fara zaman tantance mutanen a ranar Alhamis, 16 ga watan Yni na shekara ta 2022 da misalign ƙarfe 10 na safe.

Ana dai raɗe-raɗin cewa, hankali ya fi karkata a kan Gwamna Nyesom Wike na Jihar Ribas, a matsayin wanda za a ɗauka ya yi wa Atiku Abubakar abokin takara.

Sauran waɗanda ake tunanin naɗawa sun haɗa da Gwamna Ifeanyi Okowa na Jihar Delta, da Gwamna Udom Emmanuel na Jihar Akwa Ibom.

Tsohon Minista Tom Ikimi ne Shugaban Kwamitin Tantancewar, yayin da Aƙulu Sani Indabawa ya kasance Sakataren Kwamitin.

LEAVE A REPLY