Home Labaru PDP Kano Ta Zargi Ganduje Da Shirin Karya Tattalin Arzikin Jihar

PDP Kano Ta Zargi Ganduje Da Shirin Karya Tattalin Arzikin Jihar

68
0

Jam’iyyar PDP reshen jihar Kano, ta zargi gwamna Abdullahi Umar Ganduje da yi wa tattalin arzikin jihar zagon kasa sakamakon yajin aikin da ‘yan adaidaita sahu su ka yi.

A wata sanarwa dauke da sa hannun shugaban jam’iyyar Shehu Wada Sagag, PDP ta ce an san Kano da harkokin kasuwanci daban-daban, kuma sufuri shi ne babban ginshiki, inda masu adaidaita ke jigilar akalla kashi 80 cikin 100 na shige da fice a birnin.

Sanarwar ta kara da cewa, babban abu ne sanin cewa gwamnatin Ganduje ta gaza wa al’umman ta ta ko ina, musamman ganin yadda ba ta yi wa bangaren sufuri komai ba tsawon shekaru bakwai da ta yi a kan mulki.

Ta ce maimakon haka, ta lalata tsarin sufurin dalibai na Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso, yayin da Ganduje da tawagar sa su ka maida hukumar KAROTA a matsayin babbar hukumar tattara kudaden shiga maimakon ta zama hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa kamar yadda aka kafa ta.