Home Labaru Kasuwanci OPEC Za Ta Rage Yawan Man Da Najeriya Ke Fitarwa Da Kashi...

OPEC Za Ta Rage Yawan Man Da Najeriya Ke Fitarwa Da Kashi 20

99
0

Ƙungiyar Ƙasashen Masu Arzikin man Fetur OPEC da
ƙawayen ta, sun amince da rage ganguna miliyan 1 da dubu
393 na man da su ke fitarwa zuwa kasuwannin duniya a
kowacce rana.

Matakin dai, zai tilasta rage adadin man da Nijeriya ke fitarwa da sama da kashi 20 cikin 100.

Yarjejeniyar da ƙungiyar ta cimmawa bayan wani taro da ta gudanar a ƙarshen mako, ta tanadi cewa Nijeriya za ta rika fitar da ganga miliyan 1 da dubu 380 a kowacce rana daga watan Janairu zuwa Disamba na shekara ta 2024.

Ana sa ran Nijeriya za ta riƙa fitar da ganga miliyan 1 da dubu 826 zuwa miliyan 1 da dubu 747 a kowacce rana daga watanni Agusta zuwa Nuwamba masu zuwa.

Matakin da OPEC ta ɗauka na rage adadin man da ƙasashen ke fitarwa, zai shafi kuɗin shigar da gwamnatocin ƙasashen ke samu.

Leave a Reply