Home Labaru Kiwon Lafiya Muna Bukatar Karin Kashi 200 Na Albashi —Likitoci

Muna Bukatar Karin Kashi 200 Na Albashi —Likitoci

1
0

Rahotanni na cewa, Kungiyar likitoci masu neman kwarewa a
asibitocin gwamnatin Nijeriya sun dage a kan karin albashi na
kashi 200.

Kungiyar ta bayyana haka ne, makonni biyu bayan janye yajin aikin gargadi na kwanaki biyar da su ka yi domin jiran gwamnati ta yi wani abu a kan bukatun su.

A cikin wata sanarwa da ta fitar, kungiyar ta ce ba za ta amince da karin albashi na kashi 35 cikin 100 da gwamnatin da ta shude ta yi ba, sannan sauran bukatun su har yanzu ba a yi komai a kai ba.

Janye wani kudiri da ke neman hana likitocin da su ka kammala karatu a baya-bayan nan na ficewa daga Nijeriya har sai sun yi aikin shekaru biyar, da daukar likitoci aiki domin maye kwararrun da su ka daina aiki da kuma gaggauta inganta asibitocin gwamnati wasu ne daga cikin bukatun kungiyar.

Likitocin dai, su na son Shugaba Tinubu ya gaggauta warware matsalolin su, ya kuma aiwatar da matakan rage wa ‘yan Nijeriya radadin janye tallafin man fetur.