Home Labaru Oduduwa: Akwai Sabbin Tuhume-Tuhume A Kan Sunday Igboho – Malami

Oduduwa: Akwai Sabbin Tuhume-Tuhume A Kan Sunday Igboho – Malami

13
0

Gwamnatin tarayya ta yi nuni da yiwuwar daukaka kara, biyo bayan hukuncin da wata kotu a jihar Oyo ta yanke cewa a ba Sunday Igboho Naira biliyan 20 a matsayin diyya.

Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya Abubakar Malami ya
shaida wa manema cewa, gwamnati na da damar daukaka kara a
kan hukuncin, ko kuma ta shigar da sabuwar tuhuma a kan
Sunday Igboho.

Abubakar Malami, ya ce a cikin yanayi na yin biyayya ga
umarnin doka, akwai wasu hakkoki da bukatun da ke hannun
gwamnati.

Babban Lauyan, ya bayyana sabbin tuhume-tuhumen da za a iya
bijiro da su, giki kuwa har da hakkokin roko a kan hukunci, da
kuma hakkin shigar da kara domin kebe hukuncin da aka yanze
a kan doka.