Home Labaru Nasara: Jami’an Tsaro Sun Fara Samun Bayanan Sirri Daga ‘Yan Kasa A...

Nasara: Jami’an Tsaro Sun Fara Samun Bayanan Sirri Daga ‘Yan Kasa A Nijar

72
0
Rundunar hadin gwiwar G5 Sahel ta sanar da samun nasarar kama wasu ‘yan ta’adda sama da 10 a yankin iyakokin kasashen Nijer, Burkina, Faso da Mali bayan da ta bi diddigin wasu bayanan da ta samu daga al’ummar kauyukan jihar Tilabery.

Masu fafutuka suna ganin wannan al’amari a matsayin wani babban ci gaba a yaki da ta’addanci amma kuma suka ce wajibi ne hukumomi su dauki matakin kare duk wanda ya ke tsegunta bayanai na sirri.

A sanarwar da ta fitar rundunar hadin gwiwar G5 Sahel ta ce sakamakon wasu bayanan da wata bataliyar sojojin Nijer da ke da sansani a kauyen Wanzarbe na gundumar Tera ta samu daga mazauna kauyen Balley Koira sun bada damar cafke wasu ‘yan ta’adda 9 dauke da shanu 18 da babur 1 sabo ful da suke shirin batarwa a kasuwar kauyen na Balley Koira dake a tazarar km 30 a kudu maso gabashin Wanzarbe.

Wannan wata alama ce dake nunin an fara samin canjin tunani a wajen al’umar yankin da wani lokaci ake zargi da hada kai da ‘yan ta’adda inji wani mai bin diddigin al’amuran yau da kullum Ibrahim Kantama.