Home Home NUJ Ta Cire Ma’aikatan NOA Daga Jerin ‘Ya’yanta

NUJ Ta Cire Ma’aikatan NOA Daga Jerin ‘Ya’yanta

22
0
NUJ Ta Cire Ma’aikatan NOA Daga Jerin ‘Ya’yanta

Ƙungiyar ’Yan Jarida ta Nijeriya NUJ, ta cire ma’aikatan Hukumar Wayar Da Kai ta Ƙasa  daga cikin jerin ‘ya’yan ta tare da aiki da ita.

Lamarin dai ya na zuwa ne daga shugaban kungiyar ‘yan jarida ta Ƙasa Mr Chris Isuzugo, yayin wani taron wakilan ƙungiyar na ƙasa da aka gudanar a Kano.

Hakan ya biyo bayan amincewar wakilan ƙungiyar a wajen taron, yayin da za a amince da aikin shugabannin su.

Haka kuma, taron ya bayyana sabuwar dokar fitar da duk wasu  jami’an hulɗa da jama’a na ma’aikatu da sauran hukumomi, yayin da aka bayyana cewa su ba ‘yan jarida ba ne, don haka daga yanzu su ma ba ‘yan ƙungiya ne ba.