Home Labaru Ilimi NUC Ta Bankado Haramtattun Jami’o’In Digiri 49 A Nijeriya

NUC Ta Bankado Haramtattun Jami’o’In Digiri 49 A Nijeriya

1
0

Hukumar kula da jami’o’i ta Nijeriya NUC, ta tona asirin
jami’oi 49 masu bada takardar shaidar kammala Digiri na
farko da ba su da lasisi da gwamnatin tarayya.

Don haka hukumar ta ja hankulan al’umma musamman iyaye da masu neman digiri na farko, cewa an rufe makarantun saboda karya dokar harkar ilimi ta shekara ta 2004.

Matakin da hukumar NUC ta dauka kan haramtattun jami’o’in, ya nuna aniyar ta na tabbatar da ingancin tsarin ilimi a Nijeriya.

Hukumar, ta shawarci al’umma su tabbatar da matsayin kowace jami’a kafin su fara karatu a cikin ta, ta yadda za su kiyaye kokarin su na neman ilimi da makomar shi.