Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ya tabbatar da nadin
Dakta Oluwatoyin Sakirat Madein a matsayin Babbar Akanta
ta Nijeriya.
Nadin Dakta Sakirat dai ya biyo bayan samun nasarar cike tsari da ka’idojin zaben wanda zai hau kujerar ne.
Dakta Madein za ta karbi ragamar ofishin ne a hannun Mista Sylva Okolieboh, wanda ya kasance a matsayin Akanta-Janar na rikon kwarya biyo bayan dakatar da Idris Ahmed daga mukamin bisa zarge-zargen rashawa da sama da fadi da dukiyar al’umma.
Yanzu haka dai Ahmed Idris ya na karkashin shari’ar da hukumar yaki da cin hanci da rashawa EFCC bisa zarge- zargen almundahana.
Shugabar ma’aikata ta Gwamnatin tarayya Dakta Folasade Yemi-Esan ta sanar da nadin Dakta Madein a Abuja.
A cikin wata sanarwar da daraktan yada labarai na ofishin shugabar ma’aikatan Mohammed Abdullahi Ahmed ya fitar, ya ce nadin ya fara aiki ne nan take daga ranar Alhamis 18 ga watan Mayu na shekara ta 2023.