Home Labaru Nnamdi Kanu Ya Kai Ƙarar Buhari Ga Jakadun Amurka Da Na Birtaniya

Nnamdi Kanu Ya Kai Ƙarar Buhari Ga Jakadun Amurka Da Na Birtaniya

113
0

Shugaban Ƙungiyar masu rajin kafa kasar Biafra Nnamdi Kanu, ya rubuta wa Jakadar Amurka a Nijeriya, Mary Beth Leonard wasiƙa mai ɗauke da ƙorafin neman ta tura wakili domin ya zauna ya kalli zaman shari’ar da ake yi ma shi a Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja.

Nnamdi Kanu, ya kuma ya rubuta wa Jakadan Birtaniya a Nijeriya Catriona Laing wasika, inda ita ma ya roki ta aika wakilai domin su kalli shari’ar a mako mai zuwa.

Za a dai cigaba da sauraren shari’ar da ake yi wa Nnamdi Kanu bisa tuhumar sa da cin amanar ƙasa da zargin ta’addanci a ranar 18 Ga Janairu na shekara ta 2022.

Har yanzu Nnamdi Kanu ya na tsare a Helkwatar hukumar tsaro ta farin kaya DSS tun cikin watan Yuni na shekara ta 2021 bayan an kamo shi daga ƙasar Kenya.