Home Labaru Muna Matuƙar Son Yin Aiki A Nijeriya – Twitter

Muna Matuƙar Son Yin Aiki A Nijeriya – Twitter

216
0

Dandalin sada zumunta na Twitter ya bayyana jin daɗin sa game da matakin gwamnatin tarayya na dawo da ayyukan shafin a Nijeriya bayan tsawon watanni bakwai.

Kamfanin ya ce sun ji daɗi ganin cewa mutanen Nijeriya su na iya amfani da shafin Twitter a yanzu.

A cikin wani sako da ya wallafa a shafin sa, kamfanin ya ce su na matuƙar son yin aiki a Nijeriya, inda ake amfani da Twitter ta fuskar kasuwanci da sadar da al’adu da kuma tattaunawa.

A ranar Larabar da ta gabata ne, wata sanarwa daga fadar shugaban kasa ta ce Shugaba Buhari ya amince a cire haramcin amfani da Twitter a Nijeriya.

Leave a Reply