Kwamared Joe Ajaero, ya yi kiran a inganta yanayin albashi da inshora da kuma fanshon ‘yan jarida a fadin Najeriya.
Joe Ajaero, ya yi wannan kiran ne a lokacin da ya ziyarci shugaban kungiyar ‘yan jarida ta Kasa NUJ, Dakta Chris Isiguzo a nan Abuja.
Ya ce ’yan jarida na taka rawar gani wajen fafutukar kwato ‘yancin kai da dimokuradiyyar Najeriya, amma abun takaici ne yadda ake barin su,
suna rokon a biya su albashin su.
Shugaban na NLC, ya ce aikin jarida na ƙara muni a kowace rana domin kuwa an yi watsi da jin dadin ‘yan jarida bayan ’yan jarida rukuni ne na
masu gwagwarmayar kwato ‘yanci.
Ya ci gaba da cewa ‘yan jarida ba su da hutun karshen mako, ko hutu a lokacin bukukuwa, suna aiki ta hanyar sanya wasu farin ciki,
amma sai ka ga an kori dan jarida daga aiki ko a ki biyan sa albashi na shekara daya, amma sauran ‘yan jarida ba za su wallafa labari kan irin wannan rashin adalci da ake musu ba.
Ya ce yana bayar da shawarar samar da yanayin da NLC za ta rika tuntubar halin da ‘yan jarida ke ciki duk bayan shekara biyu,
domin bayar da shawara ga kafafen yada labarai kan daidaita mafi karancin albashin ‘yan jarida.
Kazalika,ya ce ya kamata a samu fansho mai gwabi ga dukkanin ‘yan jarida bayan sun yi ritaya daga aiki, haka Inshora wani
abu ne da ya kamata ‘yan jarida su ji dadin sa.
A nasa bangaren, shugaban kungiyar NUJ Dakta Chris Isiguzo ya ce kungiyar na yin kokari matuka wajen ganin an magance matsalolin da ‘yan jarida ke fuskanta.














































