Home Labaru Nijeriya Ta Amince Jiragen Emirates Su Koma Aiki

Nijeriya Ta Amince Jiragen Emirates Su Koma Aiki

109
0

Gwamnatin tarayya ta yarda jiragen kamfanin sufuri na Emirates da ke Dubai su koma jigila a kowane lokaci daga yanzu, yayin da kamfanin jirgin Air Peace da ke Nijeriya ya ce zai koma safara zuwa Dubai daga ranar1 ga watan Maris na shekara ta 2022.

Sanarwa dai ta na kunshe ne a wata wasika da hukumar kula da sufurin jiragen sama ta Nijeriya dauke da sa hannun shugaban ta Captain Musa Nuhu ta rubuta wa shugaban hukumar sufurin jirgen sama ta Hadaddiyar Daular Larabawa Saif Mohammed Al Suwaid.

Hukumar, ta ce bayan nazarin da hukumomin da abin ya shafa su ka yi a kan dokokin kariya na korona da hukumomin Dubai su ka gindaya, a yanzu Nijeriya ta amince.

Sakamakon bullar kwayar cutar korona nau’in Omicron a karshe-karshen shekarar da ta gabata, hukumomin Hadaddiyar Daular Larabawa sun takaita sufurin fasinjoji zuwa kasar daga Nijeriya da wasu kasashen Afirka 11.

Tun farko dai Nijeriya da kasar Dubai sun sasanta sabanin da aka samu a tsakanin su, game da gwajin cutar korona da kuma yawan jiragen da za su rika sufuri a tsakanin kasashen biyu.

Leave a Reply