Gwamnatin tarayya tare da hadin gwiwar hukumar kula da
Ilimi da kimiyya da al’adu ta Majalisar Dinkin Duniya
UNESCO da sauran masu ruwa da tsaki, sun fara tattaunawa
domin samun mafita game da matsalar cin zarafin mata a
makarantun Nijeriya.
Tuni dai an kafa kwamitin da zai yi nazari a fannin shari’a domin tabbatar da an hukunta masu cin zarafin yara mata a makarantun Nijeriya.
Yayin kaddamar da kwamitin a Abuja, babbar lauyar tarayyar Nijeriya kuma babbar sakatariyar ma’aikatar shari’a Mrs Beatrice Jedy-Agba, ta ce yara su na da hakkin a kare su daga duk wani nau’in tashin hankali a gida ko a makaranta.
Beatrice Jedy-Agba, ta bukaci gwamnati ta samar da kundin tsarin aikin da zai yi wa masu ruwa da tsaki a makarantu domin fuskantar duk wani batun cin zarafin da zai iya tasowa.
Ta ce kwamitin da aka kafa akan matsalaolin cin zarafin mata a makarantu, zai yi aiki tare da bangaren kula da al’amurran da su ka shafi cin zarafi domin aiki tare wajen samar da kundin da zai bada bayanan matakan da za a dauka idan aka samu aukuwar irin wadannan matsaloli a makarantu.