Home Labaru N3m Kacal Na Tarar a Asusun Zamfara – Gwamna Dauda

N3m Kacal Na Tarar a Asusun Zamfara – Gwamna Dauda

121
0

Gwamnan Jihar Zamfara Dauda Lawal Dare, ya ce Naira
miliyan uku kacal ya tarar a asusun jihar bayan ya karɓi mulki
a ranar 29 ga watan Mayu.

Dauda Lawal ya bayyana haka ne yayin hirar da sashen Hausa na BBC, inda ya ce gwamnatin da ya gada ta gaza biyan albashin ma’aikata na watanni uku a jere kafin mulki ya koma hannun sa.

Gwamnan ya cigaba da cewa, Gwamnatin da ta gabata ta bar asusun jihar a bushe babu komai a ciki, amma su na aiki tuƙuru domin bunƙasa yanayin sai dai zai ɗauki lokaci.

Dauda lawal ya kara da cewa, jihar ta gaza wajen biyan hukumomin tsaro hakkokin su a wancan lokacin, kuma ɗaliban makarantun sakandare ba su samu zarafin rubuta jarrabawar WAEC da NECO ba.

Ya ce da bashi ya ke gudanar da harkokin jihar Zamfara tun da ya karɓi ragamar mulki, domin ya tarar da asusun jihar babu kuɗi, Naira miliyan uku zuwa huɗu kawai ke ciki.

Leave a Reply