Home Home Nijar: Matakai Na Diflomasiyya Ya Kamata Ecowas Ta Dauka Ba Na Soji...

Nijar: Matakai Na Diflomasiyya Ya Kamata Ecowas Ta Dauka Ba Na Soji Ba-Atiku

95
0

Dan takarar shugaban n a jam’iyyar PDP Atiku Abubakar, ya bayyana ra’ayin sa dangane da juyin mulkin da aka yi a jamhuriyar Nijar.

Atiku Abubakar, ya ce bai goyi bayan daukar matakan soji da kungiyar ECOWAS ke shirin yi domin warware rikicin jamhuriyar Nijar ba.

Tsohon mataimakin shugaban kasar, ya kuma shawarci ECOWAS kada ta yi amfani da karfin soji  domin hakan na iya dagula al’amurra, ya na mai cewa rikicin da ke faruwa a Nijar abu ne da ke buƙatar matakan diflomasiyya ba nuna ƙarfi ba. Atiku Abubakar, ya kuma jinjina wa ƙungiyar ECOWAS bisa ƙoƙarin da ta ke yi na ganin an dawo da dimokuraɗiyya a ƙasar Nijar.

Leave a Reply