Home Home Niger: Ƴan Ta’adda Sun Ƙashe Mutum 1, Sun Tasa Ƙeyar Mutum 15...

Niger: Ƴan Ta’adda Sun Ƙashe Mutum 1, Sun Tasa Ƙeyar Mutum 15 Cikin Daji

71
0

‘Yan bindiga masu yawa sun kai farmaki karamar hukumar Rafi ta jihar Neja, a wannan karon sun kashe  mutum 1, yayin da suka yi garkuwa da sauran mutanen kauyen guda 15, wadanda yawancin su mata ne.

‘Yan ta’addan kamar yadda aka bada labari sun kai farmaki kauyen Batagari a yankin Mai-kujeri na karamar hukumar, yayin da suka bayyana a kan Babura.

Rahotanni  sun ce sun isa kauyen ne yayin da suka yi ta harbi a iska dan su jefa firgici a zukatan mazauna kauyen.

‘Yan ta’addan bayan sun razanar, suka fara yawo daga gida zuwa gida suna bincikar kowanne lungu da sako suna kwasar muhimman kayayyakin mutane.

Hukumomi daga kauyen sun ce babu iyalan da suka samu zantawa da ‘yan bindigan kuma ba su da masaniya game da inda suka kai wadanda suka yi garkuwa da su.

Har zuwa lokacin da aka tattara wannan rahoton, lambar kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Neja, DSP Wasiu Abiodun ba ta shiga.