Home Labaru Kiwon Lafiya Neman Maslaha: Za A Yi Wuraren Kiwo 368 A J Ihohi 25...

Neman Maslaha: Za A Yi Wuraren Kiwo 368 A J Ihohi 25 Na Nijeriya

74
0
Filin Kiwo

Amincewa da shugaba Muhammadu Buhari ya yi na samar da wuraren kiwo 368 a Jihohi 25 ya dauki hankalin manya manoman Nijeriya, kasar, inda wasun su ke ganin an dauko hanyar magance yawan rikicin da ke faruwa tsakanin manoma da makiyaya.

Yayin da wasu jihohi su ka nuna kin amincewa da yunkurin masu ruwa da tsaki a fannin noma kuma sun ce abu ne da ya kamata a yi tun tuni.

Matakin da shugaba Buhari ya dauka dai, ya biyo bayan shawarwarin da wani kwamitin musamman ya ba shi, wanda ya yi nuni da cewa samun wuraren kiwo zai taimaka wajen rage rikicin manoma da makiyaya.

Shugaban kungiyar manoma ta kasa Arc. Kabir Ibrahim, ya ce idan aka samu irin wanan gagarumin sauyi, ya kamata mutane su amince da shi saboda a gwada a gani.

Sai dai wasu jihohin Kudu maso Gabas, da Kudu maso Kudu da Kudu maso Yamma, da ma wasu a yankin Arewa sun sun ce ba za su amince da samar da wuraren kiwo a jihohin su, ba duk da cewa kwamitin ya ce sai an yi tuntuba tare da wayar da kan jama’a kafin a kai ga tabbatar da shi a jihohin.