Home Home NDLEA Ta Kama Mata 127 Cikin Ƴan Kwaya 1,078 Da Hukumar Ta...

NDLEA Ta Kama Mata 127 Cikin Ƴan Kwaya 1,078 Da Hukumar Ta Kama A Jihar Kano A 2022

31
0
Hukumar hana Sha da safarar miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA reshen jihar Kano, ta ce ta kama Ton 9 na miyagun kwayoyi da kudin su ya kai naira biliyan 1 da rabi, sannan ta kama masu sha da safarar kwayoyi dubu 1 da 78 cikin watanni 12 a jihar.

Shugaban hukumar Abubakar Idris-Ahmad ya sanar da haka a Kano, inda ya ce hukumar ta kai samame wurare 82 da su ka yi kaurin suna wajen sha da safarar miyagun kwayoyi ciki da wajen jihar Kano.

Ya ce sun kama mutane dubu 1 da 78 da ke da alaka da Sha ko safaran haramtattun kwayoyi, wadanda su ka hada da mata 127 da maza 951.

Idris-Ahmad, ya ce kotu ta yanke wa mutane 113 daga cikin wadanda aka kama hukunci, yayin da hukumar ta kona gonakin tabar wiwi biyar, sannan ta na kula da mutane sama da dubu 1 da 844 da ke fama da matsalolin tabin hankali sakamon tu’ammali da miyagun kwayoyi.