Home Labarai Nasara: Soji Sun Kashe Ƴan Ta’adda Dubu Takwas A Najeriya Cikin 2024

Nasara: Soji Sun Kashe Ƴan Ta’adda Dubu Takwas A Najeriya Cikin 2024

376
0
maxresdefault
maxresdefault

Rundunar sojin Najeriya ta ce ta kashe ƴan ta’dda dubu 8, da 34 daga farko zuwa ƙarshen shekara ta 2024.

Wata sanarwa da darektan yaɗa labarai na rundunar, Manjo-janar Edward Buba ya fitar, ta ce an samu nasarar ne a samame daban-daban da sojoji suka kai yankunan arewa maso gabas da kuma sauran yankunan ƙasa.

Ya ce an kama wasu ‘ƴan ta’dda’ dubu 11 da 263 da kuma ceto mutum dubu 6 da 376 da aka yi garkuwa da su.

Ya ce sun kuma samu nasarar ƙwato makamai dubu 8 da 216 da harsasai dubu 211 da 459, sun kuma daƙile yunkurin satar ɗanyen mai da kuɗin sa ya kai sama da naira biliyan 57.

Sai dai duk da irin waɗannan nasarori da rundunar sojin ke ayyanawa, Najeriya na ci gaba da fama da matsalar tsaro a yankuna daban-daban.

Ko a cikin kwanakin nan an samu ɓullar wata sabuwar ƙungiyar ƴan bindiga arewa maso yammacin Najeriyar, waɗanda ake kira Lakurawa.

Haka nan ma a baya-bayan nan ƙungiyoyin ƴan bindiga sun riƙa dasa nakiyoyi a kan hanyoyin mota a jihar Zamfara, lamarin da ya haifar da asarar rayuka da dukiyoyi.

Leave a Reply