Gwamnatin Tarayya ta fara shirin samar da wutar lantarki ga kasar Chadi daga Najeriya inda Gwamnatin Chadin ta bukaci a farfado da tattaunawar da ke tsakanin kasashen kan lamarin.
Jakadan Chadi a Najeriya, Abakar Saleh Chahaimi ne ya yi rokon yayin da ya ziyarci Ministan Wutar Lantarki Injiniya Abubakar Aliyu a nan Abuja.
Chahaimi ya ce a baya kasashen sun fara tattaunawa kan yadda Najeriya za ta rika ba wa Chadi wutar lantarki, amma ba a kai ga kulla yarjejeniyar ba.
Don haka ya roki ministan ya taimamaka wajen sake taso da maganar, domin a cewarsa, kasashen biyu za su amfana da tsarin.
Jakadan ce yarjejeniyar da Bankin Duniya ya dauki nauyi kan samar da wutar lantarki daga Kamaru zuwa Chadi zai kawo karin hadin kai da cigaba a tsakanin kasashen Afirka.
A nasa bangaren, Ministan Wutar Lantarki, Injiniya Abubakar Aliyu, ya ba da tabbacin ci gaba da maganar samar wa Chadi wutar lantarki daga Najeriya.
A cewarsa daraktocin ma’aikatarsa da ke da masaniyar inda batun ya kwana za su ci gaba da aiki a kan lamarin