Home Labaru Jiragen Emirates Za Su Ci Gaba Da Aiki A Najeriya

Jiragen Emirates Za Su Ci Gaba Da Aiki A Najeriya

202
0

Kamfanin jiragen sama na Emirates, mallakin kasar Hadaddiyar Daular Larabawa ya dawo da harkokinsa a Najeriya, bayan wata tara da daina aiki.

Emirates kamfanin jiragen sama mafi girma a duniya ya dakatar da harkokinsa a Najeriya ne bayan takun saka tsakanin gwamnatin Daular larabawa da Najeriya a kan dokokin korona.

Rikicin ya dai ya samo asali ne bayan hukumomin kasar sun wajabta yin gwajin gaggawa ga fasinjoji masu son zuwa can, baya ga shaidar rashin kamuwa da cutar da gwamnatin Najeriya ta amince da shi.

A wancan lokacin Najeriya ta yi watsi da hakan, lamarin da ya yi sanadiyyar dakatar da harkokin sufurin jirage tsakanin kasashen biyu, inda kuma yanzu aka sasanta.

A ranar Alhamis, 2 ga Disamba, 2021, ranar bikin cikar UAE shekara 50, ta sanar cewa jiragen Emirates za su ci gaba da jigilar fasinjoji a Najeriya daga ranar Litinin 5 ga watan.

Daga ranar kamfanin zai rika jigilar fasinjoji a kullum rana zuwa birnin Dubai, inda ake yawan zuwa domin hutu ko harkokin kasuwanci daga sassan duniya.

Leave a Reply