Home Home NAFDAC Ta Gargadi Masu Yin Bilicin

NAFDAC Ta Gargadi Masu Yin Bilicin

74
0
Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta Nijeriya NAFDAC, ta gargadi ‘yan Nijeriya su ƙaurace wa amfani da kayan kwalliyar da ke sauya fatar jikin bil adama daga baƙa zuwa fara.

Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta Nijeriya NAFDAC, ta gargadi ‘yan Nijeriya su ƙaurace wa amfani da kayan kwalliyar da ke sauya fatar jikin bil adama daga baƙa zuwa fara.

NAFDAC ta bayyana haka ne, a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun ta Olusayo Akintola ya raba wa manema labarai.

Hukumar, ta umarci a kama, tare da gurfanar da wadanda su ke tallata sinadarin ba tare da sahalewar hukumomin Nijeriya ba. Ta ce an haramta wadannan kayayyaki, domin su na da lahani ga fata da wasu sassan bil adama kamar hanta da koda.