Home Home Nadin Sarauta: Gwamnan Gombe Ya Nada Kwairanga Sabon Sarkin Funakaye

Nadin Sarauta: Gwamnan Gombe Ya Nada Kwairanga Sabon Sarkin Funakaye

45
0

Gwamnan jihar Gombe Muhammadu Inuwa Yahaya ya nada Alhaji Yakubu Muhammad Kwairanga a matsayin sabon Sarkin Funakaye.

Sanarwar nadin na kunshe ne a wata takarda da ke dauke da sa hannun kwamishinan ma’aikatar kananan hukumomi da lamurran masarautu, Ibrahim Dasuki Jalo.

Sabon Sarkin wanda aka haifa a ranar 1 ga watan Yulin 1981 kani ne ga marigayi Mu’azu Muhammad Kwairanga, wanda ya mutu a ranar 27 ga watan Agusta, shekara daya bayan hawansa karagar mulki.