Home Labaru 2023: ACF Ta Gargadi ’Yan Siyasa Kan Kalaman Tayar Da Hankali

2023: ACF Ta Gargadi ’Yan Siyasa Kan Kalaman Tayar Da Hankali

39
0

Ƙungiyar Tuntuva ta Arewa Consultative Forum (ACF) a ranar Lahadin da ta gabata ta gargaɗi ’yan siyasa da su guji rura wutar rikici a siyasa.

Ƙungiyar a cikin wata sanarwa da ta fitar mai taken ‘Batun ƙiyayya da tashin hankali ne za su zama mutuwarmu,’ babban sakataren ƙungiyar ta ACF, Murtala Aliyu, ya gargaɗi ‘yan siyasa da su guji furta kalamai da maganganun da ka iya jefa rayuwar ‘yan ƙasa cikin haɗari, inda ya ƙara da cewa, rashin bin doka da oda idan ba a magance shi ba zai iya haifar da rikici mai tsanani, tare da haifar da tashin hankali wanda ba zai dace da buƙatun jama’a ba.

Sanarwar ta ci gaba da cewa, baya ga rashin tsaro, wahalhalu da ƙalubale da dama da mutane ke fuskanta a halin yanzu, akwai kuma wasu ’yan siyasa da ke da ra’ayin ƙara zage damtse saboda son kai, kamar yadda ta gargaɗi waɗanda abin ya shafa da su tashi tsaye wajen yin adalci, su guji yin hakan. kowane irin mugun tunani.

“A abin kunya, makauniyar buri ne ko kuma ƙiyayya bayyananniya ke tafiyar da yawancinsu. Babu wanda zai yi ƙasa a gwiwa wajen lura da tashin hankali da rashin bin doka da oda yayin da yaƙin neman zaɓe da fafatawar ke kara taruwa. Akwai rahotannin da ke cewa wasu ’yan siyasa suna haɗa baki da ’yan daba da masu tayar da ƙayar baya domin kai wa abokan hamayya hari, suna yaɗa ta’addanci da fargaba a ko’ina,” inji sanarwar.

Har ila yau, ya qara da cewa, abin da ya fi damun ’yan siyasa masu son kai a zamanin nan, shi ne amfani da kalaman nuna