Home Labaru Ban Hana ‘Yan Shi’a Gudanar Da Addinin Su Ba – Buhari

Ban Hana ‘Yan Shi’a Gudanar Da Addinin Su Ba – Buhari

788
0
Shi'a

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya ce umarnin da kotu ta bada na dakatar da ayyukan kungiyar Shi’a bai hana mabiyan ta su gudanar da addinin su a Nijeriya ba.

Shugaba Muhammadu Buhari
Shugaba Muhammadu Buhari

Bayanin shugaba Buhari ya na zuwa ne, bayan hukuncin da wata kotun tarayya da ke Abuja ta zartar, inda ta bada umarnin haramta ayyukan Kungiyar Shi’a da ke karkashin jagorancin Sheikh Ibrahim Zakzaky kamar yadda gwamnati ta nema.

Bayanan kotun sun nuna cewa, gwamnati ta nemi a haramta kungiyar Shi’a bayan ayyana ta a matsayin ta ‘yan ta’adda, inda ta zarge ta da haifar da asarar rayuka da dukiyoyin al’umma.

Karanta Wannan: Ruga: Jahohi Ya Kamata Su Fara Shirin-Gwamna Ganduje

Sai dai mai maitamaka wa shugaban kasa ta fuskar yada labarai Garba Shehu ya shaida wa manema labarai cewa, za a aiwatar da hukuncin kotun domin haramta kungiyar Shi’a, amma ya ce hakan ba ya na nufin haramta Shi’a ba.