Home Labaru Nade-Nade: Matasa Sun Bukaci Buhari Ya Cigaba Da Boss Mustapha

Nade-Nade: Matasa Sun Bukaci Buhari Ya Cigaba Da Boss Mustapha

333
0

Gamayyar kungiyoyin matasan Nijeriya a karkashin jagorancin Kwamred Nuhu Sani Lere, ta karyata rahotannin da ke cewa gwamnatin shugaba Buhari ta yanke hukuncin mika mukamin sakataren gwamnatin tarayya ga al’ummomin kudu maso gabashin Nijeriya.

Shugaban kungiyar Kwamred Nuhu Sani Lere, ya ce wannan farfaganda ce kawai ta wasu marasa kishin kasa, domin kujerar sakataren gwamnatin tarayya cancanta ake dubawa ba matakin siyasa ba.

Nuhu Sani Lere ya cigaba da cewa, idan da so samu ne, shugaba Muhammadu Buhari ya cigaba da aiki tare da Boss Mustapha a matsayin sakataren gwamnatin tarayya, duba da irin gagarumar gudunmuwar da bada wajen tabbatar da ci-gaban kasa ta kowace fuska.

Idan dai za a iya tunawa, a baya shugaba Buhari ya sha alwashin amfani da kwarewa da kuma cancanta idan ya tashi rabon mukamai.

Don haka Kwamred Nuhu Sani Lere ya ce, idan dai cancanta da kwarewa ake bukata, babu wanda ya cancanci ci-gaba da rike mukamin sakataren gwamnatin tarayya kamar Boss Mustapha.