Home Home Mutuwar Mahsa Amini: Iran Ta Yanke Hukuncin Kisa Kan Daya Daga Cikin...

Mutuwar Mahsa Amini: Iran Ta Yanke Hukuncin Kisa Kan Daya Daga Cikin Masu Zanga-Zanga

65
0

Ma’aikatar Shari’ar Iran ta ce ta yanke hukuncin kisa na farko kan ɗaya daga cikin masu zanga-zanga a ƙasar kan rasuwar Mahsa Amini a hannun jami’an tsaro.

Ma;aikatar ba ta bayyana suna ko jinsin wanda aka yanke wa hukuncin ba sai dai ta bayyana cewa ko ma waye yana ko tana daga cikin waɗanda aka kama da laifin ƙona wani ginin gwamnati da aikata laifuka da ke barazana ga tsaron ƙasar.

Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi kira ga Iran ta daina kama mutane da laifuka waɗanda a ƙarshe za a yanke musu hukuncin kisa saboda zanga-zangar lumana da suka yi.

A shekarar 2020 mutum biyu ne aka ce an aiwatar wa hukuncin kisa a Iran sakamakon zanga-zanga.