Home Home Ta’ammuli Da Kwaya: NDLEA Ta Kama Wata Mata Da Ta Yi Niyyar...

Ta’ammuli Da Kwaya: NDLEA Ta Kama Wata Mata Da Ta Yi Niyyar Safarar Hodar Ibilis Zuwa Saudiyya

34
0

Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Najeriya NDLEA ta ce ta kama wata mata da ta yi niyyar zuwa Saudiyya da hodar ibilis a cikin wasu takalma a filin jirgin sama na Legas.

A wani saƙo da hukumar ta fitar a shafin ta na Tuwita ta ce ta kuma ƙwace hodar ibilis da nauyin ta ya kai kilogiram 5.6 da wasu ƙwayoyin da aka yi niyyar safarar su zuwa ƙasashen Australiya da Cyprus a filin jirgin maƙare cikin wasu saiwoyin doya.

Hukumar ta ce ta kama matar mai suna Ajisegiri Kehinde Sidika mai shekara 56 a filin jirgin saman birnin Legas a lokacin da take ƙoƙarin hawa jirgi zuwa Saudiyya da hodar ibilis da nauyinta ya kai kilogram 400 naɗe a cikin takalma.