Home Labarai Kasafin Kudin 2022: ‘Yan Majalisar Dattawan Najeriya Sun Amince

Kasafin Kudin 2022: ‘Yan Majalisar Dattawan Najeriya Sun Amince

225
0

Yan majalisar dattawa a Najeriya sun amince da kasafin kudin shekarar 2022 wanda shugaba Muhammadu Buhari ya gabatar musu da ya haura sama da naira tiriliyan 16.

Shugaban majalisar Sanata Ahmad Lawal ne ya sanar da hakan yayin zaman majalisar na ranar Laraba, inda ya ce sun yi aiki tare da bangaren zartaswa tare da cika alkawarin da suka dauka na amincewa da kasafin kafin hutun kirmisimeti.
Ahmad Lawal ya ce akwai wadanda ke ganin ba su iya cimma wannan wa’adi ba, amma sai ga shi majalisar na kokarin nade tabarmar wannan shekarar da nasarar cika babban alkawari.
A lokacin da ya gabatarwa ‘yan majalisar kasafin kudin, shugaba Muhammadu ya ce zai mayar da hankali wajen kammala ayyukan da gwamnatinsa ta fara a cikin kasafin na sama da tiriliyan 16.

Leave a Reply