Home Labaru Kiwon Lafiya Mutum 5 Sun Warke Daga Coronavirus A Najeriya

Mutum 5 Sun Warke Daga Coronavirus A Najeriya

777
0
Gwamnatin Legas Ta Hana Sallar Juma’a Da Taruwa A Coci Na Tsawon Makonni 4
Gwamnatin Legas Ta Hana Sallar Juma’a Da Taruwa A Coci Na Tsawon Makonni 4

Mutum biyar sun warke daga cutar Coronavirus a jihar Legas.

Gwamnatin jihar Legas ta sallami mutum biyar suka warke daga cutar ne ne daga Asibitin Cututtuka Masu Yaduwa da ke Yaba.

Gwamnan jihar Babajide Sanwo-Olu ya tabbatar da haka a cikin sanarwar da ya fitar ta shafinsa na zumunta a ranar Litinin.

Asibitin Yaba, shi ne aka mayar na killacewa tare da kula da masu COVID-19 a Najeriya.

Kawo yanzu mutum 6 ke nan suka warke daga cutar coronavirus a Najeriya.

Zuwa safiyar Litinin mutum 68 ke fama a cutar a jihar Legas inda annobar coronavirus din ta fi kamari a fadin Najeriya.

Alkaluman Cibiyar Hana Yaduwar Cututtuka (NCDC) a cikin sanarwar da ta saba fitarwa ta ce Babban Birnin Tarayya, Abuja ke biye da Legas da yawan mutum 21 masu fama da coronavirus.