Home Labarai Mutum 36 Sun Kamu Da Cutar Monkey Pox A Jihohi 14 A Nijeriya

Mutum 36 Sun Kamu Da Cutar Monkey Pox A Jihohi 14 A Nijeriya

59
0

Hukumar hana yaduwar cututtuka ta ƙasa NCDC, ta ce an samu karin mutane 141 da ake zargin sun kamu da cutar Kyandar Biri da ake kira Monkey Pox a jihohi 13 na Nijeriya.

A baya dai adadin yawan mutanen da ake zargin sun kamu da cutar sun kai 110 a Nijeriya.

Hukumar ta sanar da haka ne a shafin ta na yanar gizo, inda ta ce ya zuwa yanzu cutar ta yaɗu zuwa kasashen da ba su da tarihin an taɓa samun bullar ta.

NCDC ta ce, daga cikin mutane 141 da ake zargin sun kamu da cutar, sakamakon gwaji ya nuna cewa mutane 36 ne su ka kamu da ita a jihohi 14 da Abuja, daga ranar 1 ga watan Janairu zuwa 12 ga watan Yuni na shekara ta 2022.