Home Labaru Mutane Uku Sun Mutu A Rikicin ‘Yan Sanda Da Masu Keke Napep...

Mutane Uku Sun Mutu A Rikicin ‘Yan Sanda Da Masu Keke Napep A Legas

8
0

Mutane uku sun rasa rayukan su, bayan ‘yan sanda da masu tuƙa KEKE NAPEP sun gwabza a kan titin Command da ke Legas.

Rikicin dai ya fara ne, yayin da wani ɗan sanda mai ba ababen hawa hannu ya soka ma wani mai KEKE NAPEP wuƙa a ƙirjin sa saboda ya ƙi ba shi naira 100 da ya buƙata.

Wannan ne ya fusata sauran masu tuƙa KEKE NAPEP, inda nan take su ka bi ɗan sandan a guje amma ya tsere, don haka su ka ɗauki gawar zuwa ofishin ‘yan sanda na Meira su ka ajiye ta.

Wata majiya ta ce, masu tuƙa KEKE NAPEP sun gudanar da zanga-zanga, inda su ka yi ƙoƙarin ƙona ofishin ‘yan sandan amma aka tarwatsa su da harsasai da hayaƙi mai sa hawaye.

Rundunar ‘yan sanda ta jihar Legas, ta ce tuni kwamishinan ‘yan sanda na jihar Hakeem Odumosu ya tura jami’ai domin tabbatar da tsaro a unguwar da lamarin ya faru.