Home Labaru Mutumin Da Ya Dare Fuffuken Jirgi A Legas Ba Dan Nijeriya Ba...

Mutumin Da Ya Dare Fuffuken Jirgi A Legas Ba Dan Nijeriya Ba Ne – FAAN

489
0

Hukumar kula da filayen tashi da saukar jiragen sama ta Nijeriya FAAN, ta ce mutumin nan da ya dare a fuka-fukan jirgin saman kamfanin Azman tare da hana shi tashi a filin jirgin sama na Murtala Mohammed dan asalin kasar Nijar ne ba dan Nijeriya ba.

Karata Wannan: Sufuri: Buhari Ya Amince Da Nadin Yadudu A Matsayin Sabon Shugaban Hukumar FAAN

Fasinjojin da ke cikin jirgin da zai kai su Fatakwal dai sun shiga dimuwa, bayan sun hango mutumin mai suna Usman Adamu ya yi dare-dare a kan daya daga cikin fuka-fukan jirgin da su ke ciki yayin da ya ke niyyar tashi sama.

Adamu dai ya yi yunkurin shiga dakin ajiye kaya na jirgin, lamarin da ya tilasta direban jirgin kashe injin jirgin, ya kuma fasa tashi sama kamar yadda ya yi niyya da farko.

Babban manajan hukumar FAAN da jami’in hulda da jama’a Henrietta Yakubu sun tabbatar da cewa, mutumin dan asalin kasar Nijar ne da hukumar ta kama kwana biyar da su ka wuce saboda yin kutse a filin jirgin sama.

Tuni dai hukumar FAAN ta dakatar da manyan shugabannin bangaren tsaro hudu har zuwa lokacin da za a kammala binciken yadda aka yi sakaci mutumin ya kai ga zuwa wurin da jirgi ke tashi tare da dare fuffuken sa.