Home Labaru MURIC Ta Faɗi Sunayen Yarbawa Musulmai Da Ta Ce Sun Cancanci Rike...

MURIC Ta Faɗi Sunayen Yarbawa Musulmai Da Ta Ce Sun Cancanci Rike Nijeriya

16
0

Kungiyar kare haƙƙin Musulmi ta Nijeriya MURIC, ta jaddada goyon bayan ta ga fifita ɗan takarar shugaban ƙasa ya kasance musulmi kuma ɗan ƙabilar Yarabawa.

A cikin wata sanarwa da aka raba wa manema labarai, MURIC ta ce babu wani musulmi Bayarabe da ya taɓa rike mukamin shugaban ƙasa ko mataimakin sa tun samun ‘yancin Nijeirya a shekara ta 1960.

Ƙungiyar, ta bayyana Yarabawa Musulmai guda takwas da ta ce sun cancanci su jagoranci Nijeriya, wadan da su ka hada da Bola Tinubu da Ishaq Oloyede da Muiz Banire da mataimakin gwamnan jihar Legas Dr. Kadiri Obafemi Hamzat.

Sauran sun hada da tsohon gwamnan jihar Legas kuma ministan ayyuka da gidaje Babatunde Fashola, da tsohon gwamnan jihar Osun kuma ministan harkokin cikin gida Rauf Aregbesola.