Home Labaru Mun Tsara Yadda Tinubu Zai Janye Tallafin Fetur – Boss Mustapha

Mun Tsara Yadda Tinubu Zai Janye Tallafin Fetur – Boss Mustapha

91
0

Gwamnatin tarayya, ta ce ta tsara wani kundi da zai taimaka
wa sabuwar gwamnati a kan yadda za ta cire tallafin mai ba
tare da kalubale ba.

Ta ce ta yi iyakar kokarin ta wajen ganin ta tafiyar da harkokin tallafin mai duk kuwa da tarin kalubale, sannan ta sanar da kashe Naira tiriliyan 13 daga shekara ta 2005 zuwa 2021.

Yayin wani taro da aka gudanar a Abuja, Sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha, ya ce gwamnatin tarayya ta na bibbiyar abubuwan da ake faɗi game da janye tallafin Mai.

Ya ce daga cikin abubuwan da ake tattaunawa akwai bukatar gyara matatun man Nijeriya da samar da shirin da zai rage wa mutane radadin janye tallafin musamman talakawa da ma’aikata.

Boss Mustapha na jadadda cewa, su na da kwarin gwiwar sabuwar gwamnatin da za a rantsar za ta gudanar da ayyuka da kuma yanke hukunci ba tare da cutar da al’umma ko jefa su cikin matsi ba.

Leave a Reply