Home Labaru Mun Sauya Fasalin Kuɗi Ne Don Maganin Waɗanda Suka Ɓoye Kuɗin Haram...

Mun Sauya Fasalin Kuɗi Ne Don Maganin Waɗanda Suka Ɓoye Kuɗin Haram – Buhari

20
0
Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya ce gwamnati za ta tabbatar da cewa ‘yan Nijeriya ba su wahala ba ta fuskar kasuwanci da kuma samun tsaiko wajen musanya tsofaffin takardun kuɗinsu da sabbi, yayin da wa'adin da babban bankin Nijeriya ya sa ke ƙara ƙaratowa.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya ce gwamnati za ta tabbatar da cewa ‘yan Nijeriya ba su wahala ba ta fuskar kasuwanci da kuma samun tsaiko wajen musanya tsofaffin takardun kuɗinsu da sabbi, yayin da wa’adin da babban bankin Nijeriya ya sa ke ƙara ƙaratowa.

Buhari ya bayyana haka ne, yayin da ya ke maida martani game da rahotonni a kan dogayen layukan mutanen da ke shafe sa’o’i domin musanya tsofaffin kuɗinsu a bankuna, lamarin da ya janyo suka daga ɓangarorin adawa.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasa Garba Shehu ya fitar, Buhari ya ce an fito da batun sauya fasalin kuɗin Nijeriya ne don a yi maganin mutanen da su ka ɓoye kuɗin haram ba don cutar da talaka ba.

Ya ce hakan zai magance matsalar cin hanci da rashawa da ɗaukar nauyin ta’addanci da satar mutane domin karɓar kuɗin fansa, kuma tsarin zai taimaka wajen ƙarfafa tattalin arzikin Nijeriya.

Game da wahalhalun da talakawa ke sha na musanya kuɗaɗen su kuwa, shugaba Buhari ya ce gwamnati za ta yi bakin ƙoƙarin ta domin taimaka masu wajen musanya kuɗaɗen su.