Home Labaru Cece-Kuce: Shugaba Buhari Ya Rattaba Hannu Kan Dokar Man Fetur

Cece-Kuce: Shugaba Buhari Ya Rattaba Hannu Kan Dokar Man Fetur

66
0
Kudurin Man Fetur

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya rattaba hannu a kan Kudurin Dokar Man Fetur mai taken (PIB) mai cike da cece-kuce.

Shugaban kasan ya sanya hannun ne ranar Litinin din nan, kamar yadda mai Magana da yawun sa Femi Adesina ya tabbatar a cikin wata sanarwa.

Shugaba Buhari, ya ce yin hakan na daya daga cikin sauke alhakin da Kundin Tsarin Mulkin kasa ya dora masa.

Kudurin dai na kunshe da sassa guda biyar da suka hada da shugabanci da hukumoni, da gudanarwa, da raya yankunan da ke da arzikin mai, da tsara hanyoyin kashe kudaden mai, da kuma sauran tanade-tanade a cikin sadarori 319 da kuma bangarori guda takwas.

Sanarwar ta ce za a gudanar da bikin sabuwar dokar a hukumance ranar Laraba, lokacin da kwanakin killace kai na tilas da Shugaban ke yi za su cika.

Tun da farko dai Majalisar Dokoki ta Kasa ta amince da kudurin ya zama doka, duk kuwa da yadda ya jawo cece-kuce matuka da kuma tayar da kura.