Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jaddada kudirin sa na goyon bayan jamhuriyar Sahrawi Arab domin ganin ta zama kasa mai cin gashin kan ta.
Buhari ya bayyana hakan ne a lokacin da ya karbi bakuncin shugaban kasar Brahim Ghali a fadar sa da ke Abuja, inda ya kara da cewa tsayuwar Nijeriya wajen neman ‘yancin kasar Sahrawi Arab ya yi dai-dai da manufar kungiyar kasashen Afrika da majalisar dinkin duniya.
Mai Magana da yawun shugaban kasa Femi Adesina ya tabbatar da haka ga manema labarai, jim kadan bayan ganawar shugaban kasa Buhari da shugaba Barhami Ghali.
Tun da farko dai, shugaba Barhami Ghali ya taya shugaba Buhari murnar sake lashe zaben shugaban kasa da ya yi a karo na biyu, da kuma kammala bikin tunawa da ranar dimokradiyya lami lafiya.
Barhami ya kuma yabawa kokarin gwamnatin Nijeriya na ganin ksar Sahrawi Arab ta samu ‘yancin kan ta tun lokacin mulkin Buhari na soji, inda ya ce goyon bayan Nijeriya na da matukar muhimmanci wajen kubutar da al’ummar kasar daga mulkin mallaka.
You must log in to post a comment.