Home Labaru Ci-Gaba: An Nada Sarkin Kano Shugaban Jami’ar Jihar Ekiti

Ci-Gaba: An Nada Sarkin Kano Shugaban Jami’ar Jihar Ekiti

343
0

Gwamnatin Ekiti ta nada mai martaba Sarkin Kano Muhammadu Sunusi II a matsayin sabon shugaban jami’ar jihar jihar.

Wata Majiya ta ruwaito cewa, wata takarda da ke dauke da sa hannun matawallen Kano, Aliyu Ibrahim Ahmed daya aika wa sakataren gwamnatin jihar Ekiti, ta bayyana gamsuwar mai martaba Sarki da wannan mukami.

Matawallen Kano ya ce, mai martaba Sarki Sunusi ya bayyana godiyar sa ga gwamnatin Ekiti da ta duba dacewar sa da wannan mukami mai muhimmanci na jagorantar hukumar gudanarwar jami’ar jihar.

Mai martaba Sarkin Sunusi ya yi alkawarin bada gudunmuwa domin ganin martabar jami’ar ya daukaka tare da samun cigaba mai daurewa ta yadda zata amfani al’ummar jihar dama na kasa baki daya.

Idan dai za’a tunawa, a kwanakin baya ne hukumar gudanarwar jami’ar gwamnatin tarayya da ke Bini jihar Edo ta nada Sarki Sunusi a matsayin shugaban majalisar gudanarwar jami’ar, sannan kuma sabuwar jami’a mai zaman kanta da ke jihar Kano, ta Skyline ta nada shi makamancin irin wannan mukami.