Home Home Mukaman Ministoci: Shugaba Tinubu Ya Mika Sunaye Ga Majalisar Dattawa

Mukaman Ministoci: Shugaba Tinubu Ya Mika Sunaye Ga Majalisar Dattawa

94
0

Shugaban Majalisar Dattawa, Godwill Akpabio ya tabbatar da cewa shugaban kasa Alhaji Bola Ahmed Tinubu, ya gabatar da sunayen mutum 28 da yake neman a tantance domin naɗa su muƙaman ministoci.

Da yake karanto takardar a zauren majalisar Godwill Akpabio,  ya ce sunayen da shugaban kasa ya mika musu sun kunshi   Abubakar Momoh, da Yusuf Maitama Tuggar, da Ahmad Dangiwa, da Hannatu Musawa, da Uche Nnaji, da Betta Edu, da Dr. Diris Anite Uzoka, da David Umahi, da Ezenwo Nyesom Wike, da Muhammed Badaru Abubakar, da Nasir El Rufai, da Ekerikpe Ekpo, da Nkiru Onyejiocha, da Olubunmi Ojo.

Sauran sun hada da Stella Okotete, da Uju Kennedy Ohaneye, da Bello Muhammad Goronyo, da Dele Alake, da Lateef Fagbemi, da Mohammad Idris, da Olawale Edun, da Waheed Adebanwa, da Iman Suleman Ibrahim, da Prof Ali Pate, da Prof Joseph Usev, da Abubakar Kyari, da John Enoh, sai kuma Sani Abubakar Danladi.

Leave a Reply