Home Home Mukaman Kwamishinoni: Majalisar Kaduna Ta Amince Da Sunan Mutum 13 Da Aka...

Mukaman Kwamishinoni: Majalisar Kaduna Ta Amince Da Sunan Mutum 13 Da Aka Mika Mata

38
0

Majalisar Dokokin jihar Kaduna ta tantance tare da amincewa da sunan mutum 13 daga cikin 14 da gwamnan jihar Malam Uba Sani ya aike mata.

Shugaban majalisar, Honarabul Yusuf Dahiru Liman, y ace daman majalisar ta amshi sunan mutum 14 ne da gwamnan ya aike mata domin tantance su.

Ya ce wadanda majalisar ta tabbatar da nadin su a matsayin kwamishinonin a jihar Kaduna, su ne Aminu Abdullahi Shagali, da Umma Kaltume Ahmed, da Mukhtar Ahmed, da Arch. Dr.Ibrahim Hamza, da Sule Shua’ibu, da Shizzer Nasara Joy Bada, da Professor Muhammad Sani Bello, da Salisu Rabi, da Professor Benjamin Kumari Gugong, da Abubakar Bubba, da Sadiq Mamman Lagos, da Murtala Muhammad Dabo da kuma Patience Fakai.

Mutum guda daga cikin sunayen, Auwal Musa Shugaba, bai samu tantancewa da amincewar majalisar ba sakamakon gaza bayyana a zauren majalisar.

Bayan kammala aikin tantancewar, shugaban kwamitin yada labarai na majalisar, Hon. Marah Henry Zachariah, ya ce, bisa kyawawan tarihi da zababbun suke da shi, za su tabbatar da yin ayyuka masu nagarta wajen sauke nauyin da ke kan su.

Leave a Reply