Home Home Duba Koke: Shugaba Tinubu Ya Roki Kungiyar Kwadago Ta Ba Shi Karin...

Duba Koke: Shugaba Tinubu Ya Roki Kungiyar Kwadago Ta Ba Shi Karin Lokaci

39
0

Shugaban kasa Alhaji Bola Ahmad Tinubu, ya yi kira ga kungiyoyin kwadago su kara ba shi lokaci domin duba        koke- koken su kafin fara yajin aikin da suka shirya shiga.

Shugaban majalisar wakilai Tajudeen Abbas, ya bayyana rokon da shugaban kasan ya yi ga menema labarai a fadar shugaban kasa bayan da ya jagoranci wasu jami’an majalisar domin su yi wa shugaban kasa bayanin sakamakon zaman da suka yi da kungiyar Likitoci ta kasa, wadda ta shiga yajin aikin sai baba ta gani.

AbbasTajudeen ya ce, shugaba Tinubu ya roke su cewa kasancewar sa sabo a kan mulki, yana bukatar karin lokaci domin tantance batutuwan da ma’aikata suka gabatar a kai wanda har yanzu ba a yi masa cikakken bayani ba.

A ranar Larabar da ta gabata ne dai ƙungiyar ƙwadago ta bayyana shirin fara yajin aikin gargadi na kwana bakwai daga ranar 2 ga watan Agustan 2023.

Leave a Reply