Home Labaru Ilimi MSSN Ta Yi Ƙorafi Kan ‘Wayon’ Koyar Da Ɗalibai Ilimin Jima’i A...

MSSN Ta Yi Ƙorafi Kan ‘Wayon’ Koyar Da Ɗalibai Ilimin Jima’i A Nijeriya

99
0

Ƙungiyar ɗalibai Musulmi ta Nijeriya MSSN, ta rubuta wa
gwamnatin tarayya takaddar ƙorafi a kan wasu littattafai da
ake koyarwa a makarantun Nijeriya, cewa su na ɗauke da
abubuwan da za su bata tarbiyya da addinin yara.

A wasikar da kungiyar shiyya ta biyu ta aike wa Ministan Ilimi Adamu Adamu, ta ce wasu daga cikin littattafan koyar da lissafi da Ingilishi da kimiyyar zamantakewa da ake amfabi da su a yawancin makarantun sakandare, su na dauke da abubuwa na koyar da badala da batsa, wadanda ta ce an tsara su ne domin a gurbata dabi’ar matasa dalibai.

Wasikar dai ta na dauke ne da sa hannun babban jami’in kungiyar Qaasim, da Babban Sakataren ta Abdul Jalil Abdur Razaq.

Kungiyar ta ce wasu daga cikin littattafan su na yada ilimin zubar da ciki da luwadi da madigo da amfani da kororo roba da sauran dabi’u da kungiyar ta ce ba su dace da matasa ba, domin za su bata masu tarbiyyar addini da al’ada.

A karshe kungiyar ta bukaci ma’aikatar ilimi ta gaggauta gudanar da bincike a kan duk littattafan da ake amfani da su a makarantun Nijeriya, ta tabbatar ba su dauke da abubuwan da za su bata tarbiyyar dalibai matasa.