Home Labaru Labarun Ketare Mount Da Hojlund Sun Kusa Dawowa Taka Leda A United

Mount Da Hojlund Sun Kusa Dawowa Taka Leda A United

238
0
GettyImages 2153137446
GettyImages 2153137446

An samu ƙarin labarin da zai sake kwantar wa magoya bayan Manchester United hankali bayan nasarar da suka samu a kan Barnsley da ci 7-0 a tsakiyar mako.

La barin kuwa shi ne Mason Mount da Rasmus Hojlund duk sun dawo sun fara atisaye a kungiyar.

Kocin United Erik ten Hag ya bayyanawa manema labarai gabannin tafiyar United zuwa Crystal Palace a ƙarshen wannan makon,

duk da dai bai yi bayani kan ko ƴan wasan za su iya shiga tawagar da za ta yi wasa a Selhurst Park ba.

Mount ya sami rauni ne a wasa na biyu na gasar Premier a Brighton, yayin da shi kuma Hojlund ya samu rashin sa’a tun a wasan share fage da Arsenal a Los Angeles a watan Yuli.

United tana mataki na 10 a kan teburin premier na bana bayan ta ci wasa biyu ta kuma yi rashin nasara a guda biyu cikin wasanni huɗun da ta buga ya zuwa yanzu.

Leave a Reply