Hukumomi a ƙasar Italiya sun ce sun gano gawa ta shida daga cikin tarkacen jirgin ruwan alfarma, wanda ya nitse a gaɓar tsibirin Sicily sanadiyyar wata mummunar guguwa.
A wani bayani da suka wallafa a shafin sada zumunta, masu aikin ceton sun ce an gano gawar ta ƙarshe ne a ƴan sa’o’in da suka gabata,
wanda hakan ke nufin an kammala gano dukkanin gawarwakin.
Ana kyautata zaton cewa gawar ta Hannah Lynch ce, wato ƴar attajirin nan mai harkar ƙirƙire-ƙirƙiren zamani, Mike Lynch.
Attajirin na cikin mutane bakwai da yanzu aka tabbatar da mutuwar su a nitsewar jirgin ruwan na alfarma, wanda ya nitse a ranar Litinin.














































