Home Labaru Miyetti Allah Ta Sanar Da Ɓacewar Mataimakin Shugaba Na Ƙasa, Lamiɗo

Miyetti Allah Ta Sanar Da Ɓacewar Mataimakin Shugaba Na Ƙasa, Lamiɗo

444
0

Ƙungiyar Fulani Makiyaya ta Miyetti Allah, ta sanar da
ɓacewar Mataimakin Shugaban ta na Ƙasa Injiniya Munnir
Atiku Lamido.

Mai magana da yawun ƙungiyar na ƙasa Alhaji Muhammad Nura Abdullahi ya sanar da haka a cikin wata sanarwa da ya fitar, inda ya ce su na sanar da al’umma da hukumomin tsaro cewa Injiniya Munnir Atiku Lamiɗo ya ɓace.

Ya ce Injiniya Munnir ya bar gidan sa da ke Katsina ranar Juma’a, 23 ga watan Yuni da nufin zuwa Kaduna, amma har zuwa yanzu ba a san inda ya ke ba.

Sanarwar ta nuna cewa, a ranar Alhamis aka gano motar Lamiɗo a hanyar tsakanin Jos da Kaduna kusa da garin Mararraban Jos ajiye a gefen hanya da woyoyin sa duk a ciki, amma har yanzu ƙoƙarin da aka yi domin gano shi ya ci tura.

Leave a Reply