Home Labarai Miyagun Laifuka: Rundunar ‘Yan Sanda Ta Cafke Sojan Gona A Legas

Miyagun Laifuka: Rundunar ‘Yan Sanda Ta Cafke Sojan Gona A Legas

29
0

Rundunar ’Yan Sandan jihar Legas, ta kama wani sojan gona
wanda sojoji ke nema ruwa a jallo a jihar.

Kakakin rundunar, SP Benjamin Hundeyin ne, ya tabbatar wa Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN), Hundeyin, ya ce an kama wanda ake zargin ne lokacin wani samame da rundunar ta kai rukunin gidaje na Fagbile.


Ya kara da cewa sojan gonan da ya kware wajen amfani da kakin soja, inda yake aikata munanan laifuka. Ba tare da bata lokaci ba muka aika a kira Kwamandan dakarun soji domin tafiya da wanda ake zargin, inda suka tabbatar da cewa sojan gona ne. A yayin da ake yi masa tambayoyi, wanda ake zargin ya tabbatar da cewar shi ba sojan gaske ba ne.

Leave a Reply