Home Labarai Caccakar Uba Sani: Jam’Iyyar APC Ta Dakatar Da Shugabar Matan Jam’Iyyar

Caccakar Uba Sani: Jam’Iyyar APC Ta Dakatar Da Shugabar Matan Jam’Iyyar

41
0

Jam’iyyar APC a Jihar Kaduna ta dakatar da shugabar matan
jami’yyar, Maryam Suleiman, kan sukar gwamnan jihar, Uba
Sani.


Takardar dakatarwa mai kwanan watan 31 ga watan Maris mai dauke da sa hannun shugaban jam’iyyar APC da sakataren gundumar Badarawa/Malali, Ali Maishago da Zakkah Bassahuwa, ta ce an dakatar da shugabar matan ne bisa zargin bata sunan Gwamna Uba Sani, da kuma tada zaune tsaye a jami’yyar.


Ana zargin ta ne ta aike wa da ‘yan daba su kai wa mai bai wa gwamna shawara kan harkokin siyasa, Manzo Maigari hari. Takardar ta nuna cewa matakin da shugabar matan ta dauka ya saba wa sashe 21, 2 (v) na kundin tsarin jami’yyar APC. A wani faifan bidiyo da ta yi cikin harshen Hausa, shugabar matan jam’iyyar APC ta soki kalaman Gwamna Sani kan dimbin bashin da gwamnatin tsohon gwamnan jihar, Nasir El-Rufai ta bari.


 A jawabin da ya yi wa masu ruwa da tsaki a taron da aka gudanar a ranar Asabar, Gwamna Sani ya ce ya gaji bashin da ya kai dala miliyan 587, da Naira biliyan 85, da kuma bashin kwangilolin 115 daga gwamnatin El-Rufai.

Leave a Reply