Home Labarai Miyagun Ayyuka: Masu Garkuwa Sun Sace Ɗalibai 3 A Jami’Ar Kalaba

Miyagun Ayyuka: Masu Garkuwa Sun Sace Ɗalibai 3 A Jami’Ar Kalaba

45
0

       

Wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun yi awon
gaba da dalibai uku da ke karatu a Jami’ar Kalaba, fadar
gwamnatin jihar kuros Ribas

Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Ribas, Sufritanda Irene Ugbo ya tabbatar da faruwar lamarin.


Ya ce an sace ɗaliban Jami’ar Kalaba su uku a daren Ranar Alhamis, a ɗakunansu kwanansu da ke cikin jami’ar Kawo yanzu dai Ugbo bai ba da cikakken bayani dangane da satar daliban ba, sai dai ya tabbatar da cewa rundunarsu da sauran jami’an tsaro a jihar suna iya bakin ƙoƙarinsu domin ceto waɗanda lamarin ya shafa.


Wata majiya ta bayyanawa Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya NAN cewa an sace Ojang Precious Ebejin, dalibin aji biyu da ke karatu a sashen nazarin likitanci.


An kuma sace Ugwu Chukwuemeka, dalibin aji 3 da ke karatu a sashen nazarin kimiyyar halittu sai kuma Damilola Dickson, da ke shekarar karshe, duka dai daga wannan sashe.

Leave a Reply